A wani bangare na wannan taro, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa na isar da gaisuwar Jagoran juyin juya halin Musulunci ga al'ummar kasar Lebanon masu tsayin daka ya bayyana cewa: Sayyid Hasan Nasrullah zai ci gaba da kasancewa a cikin zukatan musulmi da muminai, irin wadannan muminai wadanda ya bayyana su a matsayin mutane mafi daukaka da aminci. Ya shugaban shahidan gwagwarmaya, ka tabbata cewa ‘ya’yan gwagwarmayar suna kan tafarkin tsayin daka har zuwa samun nasara akan sahyoniyawa da ma'abuta girman kai, har sai sun 'yantar da kasar Palastinu gaba daya tare da mayar da birnin Kudus ga ma'abotanta, sannan har zuwa lokacin da musulmi za su yi salla a birnin Kudus cikin nasara da alfahari.
Ayatullah Mohsen Araki ya kara da cewa: Ku tabbata nasara taku ce, nasara za ta zo, ku tabbata cewa nasara tana kan hanya, ya ku al'ummar Palastinu, ya ku masu gwagwarmayar Musulunci a Palastinu, ku ci gaba da gwagwarmaya da tsayin daka a kan tafarkinku domin nasara za ta zo, Gaza kuma za ta yi nasara, sannan sahyoniyawa za su halaka, kuma za a ci gaba da fatattakar su.
Taron ya ci gaba da jawabin Sheikh Naim Qassem, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wanda jawaban na sa ke tare da shauki daga mahalarta taron. Ya kuma jinjinawa babban matsayin da shahidan suke da shi ta hanyar girmama tunawa da sunayen manyan sakatarorin Hizbullah na kasar Labanon.
Sheikh Na'im Qassem ya yi magana ga shahidi Mujahidan Sayyid Hassan Nasrallah ya ce: Ya kai Shahidi ka bar duniya, amma ka bar mana haske ga hanya. Ana jin kasancewar ku a yau fiye da kowane lokaci; ka kasance babban shugaba kuma yanzu ka zama abin zaburarwa ga shugabannin duniya.
Kun yi yunkuri da tafya bisa koyarwar Musulunci, kun yi sadaukarwa don Allah da halittunsa, kun yi riko da umarnin Manzon Allah (SAW) da tsarkakan Imamai (SAW).
Kun yi riko da igiyar Ubangiji kuma tafarkinku ya haskaka da taimakon Allah. Kun tsaya tare da kauna tare da Imam Khumaini (RA) da biyayya ga Waliyyin Musulmi Imam Khamenei (AS). Burinku shine ku mika tutar gwagwarmaya ga Jagoran Zamani (Af).
Kai ne wanda ya assasa tafarkin Hizbullah; hanyar da za ta yi nasara da yardar Allah. Duk wanda ya dogara ga Allah da Manzonsa, zai yi nasara, kuma Hizbullah za ta yi nasara da taimakon Allah.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon ya kara da cewa: Rasuwar Sayyid Hasan Nasrallah abu ne mai matukar bakin ciki da tsananin wahala, amma haskensa da tasirinsa suna nan daram, kuma kasancewarsa a ruhinsa ya bunkasa bayan tafiyarsa. Ya kasance shugabaa wani lokaci, amma yanzu kuma ya kasance mai zaburar da shugabanni. Sayyid ya kasance “mai dauke da tutar gwagwarmaya” kuma ya dasa al’amarin Palastinu a zukata, kuma wannan shuka a yanzu ta zama gwagwarmaya mai karfi da alfahari wanda ya kafa harsashin nasara.
Sheikh Naim Qassem ya kuma girmama tunawa da girmamawa ga shahidi Sayyid Hashem Safiyudden inda ya ce: Wannan ita ce zagayowar ranar shahadar Sayyid Hashem Safiyudden. Shi ne na hannun daman Sayyid Hasan Nasrullah, ya kuma yi sadaukarwa da yawa da kuma sadaukarwa a ayyuka daban-daban, ciki har da fara gudanar da ayyukansa a yankin kudu. Dukkan hidimominsa sun tafi ne a tafarkin Allah da daukaka kalmar gaskiya da karfafa gwagwarmaya.
Sayyid Hashem ya ba da kulawa ta musamman ga tarbiyyar akida da tarbiyyantar da Mujahidan, ya kuma san cewa mafarin kowane tafarki daga zuciya da tunani ne; Don haka ne ya mayar da hankali wajen shiryawa da ilmantar da matasa da mata da kuma tallafawa iyalai gami da ‘ya’yan shahidai. Ayyukansa na zamantakewa da kiwon lafiya suna nuna karimcinsa da sadaukarwa. Ko da yake ya bar mu da wuri, ayyukansa da makarantarsa suna masu dawwama, kuma alkawarinmu ga tafarkinsa matabbaci ne kyam.
Sheikh Naeem Qassem ya ce dangane da makirce-makircen da ake tafkawa dangane da makaman gwagwarmaya: Mun tsaya tsayin daka wajen fuskantar yakin duniya wanda manufarsa ita ce ruguza gwagwarmaya da kokarin share fagen samar babbar Isra'ila. Amma makiya shun sha kayi ba su yi nasara ba, kuma a shirye muke mu yi tsayayya da duk wani mai mamaya. Haka nan za mu tunkari yakin kwance damarar makamai da salon Karbala.
Dangane da irin rawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take takawa wajen bayar da goyon baya ga gwagwarmayar ya kara da cewa: Al'ummar Iran da jagora da gwamnatin Iran tare da goyon bayansu sun sanya gwagwarmaya ta ci gaba da tafiya a kan tafarkinta. Muna kuma jinjinawa kasar Yemen, wacce ta biya farashi mai yawa don martabar gwagwarmaya. Za mu fuskanci yunkurin kwance damarar makamai kamar Karbala kuma za mu hada hannu da hannun da sojojin kasar Labanon don tunkarar babban makiyinmu.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah, yayin da yake jaddada alkawarinsa da mayakansa da masu goyon bayan gwagwarmayar ga shahidai ya ce: A madadin kaina, 'yan uwana, da wannan kungiya ta masoya, da duk masu kaunarta a fadin duniya, ina jaddada cewa, za mu ci gaba da cika alkawarin da muka dauka, Ya Nasrallah, muna maimaita wannan alkawari har sau uku: za mu ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.
Za mu ci gaba a kan wannan tafarki bayan rashin ku; Salonku da hanyarku ta ci gaba kuma za mu bi ta. Mu ne ma'abota amana, ma'abuta addinin Musulunci, tsayin daka da gwagwarmaya, da 'yancin Palastinu, kuma mun tsaya tsayin daka wajen yin riko da wannan amana.
Shekh Naeem Qassem: Mun Shirya Don Shahada; Ba Za Mu Bar Fagen Ba Kuma Ba Za Mu Ajiye Makamanmu Ba. Kamar Yadda Ka Koya Mana, Muna Ta Maimaita Cewa: "Ya Husaini, Ba Za Mu Bar Ka Ba".
Idan dai ba a manta ba a wannan rana ta shekarar da ta gabata an kai wani hari mafi girma da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a birnin Beirut, in da sakamakon harin da Sayyid Hasan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi shahada tare da wasu kwamandojin kungiyar Hizbullah da dama da kuma Janar Abbas Nilforosh daya daga cikin kwamandojin dakarun kare juyin.
Your Comment